Magoya Bayan Shugaba Ouattara Da Ke Nijar Na Ci Gaba Da Zuga Shi

Shugaba Alassan Ouattara

Magoya bayan jam’iyar RHDP ta Shugaban kasar Cote D’ivoire Alassan Ouattara, na ciki da wajen kasar, na ci gaba da kiransa ya tsaya a zaben 31 ga watan Oktoba mai zuwa domin neman wa’adin  mulki na 3, duk kuwa da cewa ‘yan hamayya na ganin rashin dacewar hakan.

Wannan ya sa masu bin diddigin al’amuran yau da kullum jan hankula game da abubuwan da ka iya biyo bayan wannan yunkuri a kasar da har yanzu ba ta kammala murmurewa ba daga rikicin da ya biyo bayan zaben shekarar 2010.

Tun a washe garin rasuwar mutumin da jam’iyyar RHDP ta tsayar a matsayin dan takararta na zaben Oktoban 2020 wato Frai Minista Amadou Gon Coulibaly, magoya bayan Alassan Ouattara suka soma kiransa ya shiga wannan fafatawa domin neman wa’adin mulki na 3.

Mutane da dama daga cikin ‘yan Cote D’ivoire mazauna Niger a karkashin jagorancin karamin jakadansu, Victor Akesse sun bayyana ra’ayi mai nuna goyon baya ga Shugaba Ouattara a wata sanarwar da suka fita.

"Ya kamata Alassan Ouattara ya shiga wannan zabe domin ya zarce akan karagar mulki, mu magoya bayan RHDP dake Nijer muna goyon bayansa domin shi kadai ne ke iya lashe zabe tun a zagayen farko da kashi 65 zuwa 70 daga cikin 100 na kuri’u."

Da yake maida martani Shugaban ya ce ba zai bayyana matsayinsa ba a halin yanzu sakamakon zaman makokin rasuwar Gon Coulibaly, to amma masu sharhi akan al’amuran yau da kullum irinsu Alkassoum Abdourahaman na cewa salo ne irin na gogaggen dan siyasa.

A can baya Shugaba Alassan Ouattara ya yi barazanar shiga zaben na 31 ga watan Oktoba muddin takwarorinsa irin Henri Konan Bedie na jam’iyar PDCI suka nuna sha’awar shiga wannan fafatawa kafin daga bisani jam’iyarsa ta RHDP ta damka tikiti a hannun Amadou Gon Coulibaly.

A karshen makon jiya, daya daga cikin manyan jam’iyun da suka kafa jam’iyar RHDP wato UDPCI ta bada sanarwar ficewa daga wannan hadaka kuma tuni ta tsayar da dan takararta na zaben dake tafe yayinda a nasa gefe tsohon Shugaban kasa Laurent Bagbo ke shirye shiryen komawa gida bayan shafe shekaru 10 a hannun kotun ICC .

Saurari cikakken rahoton da Souley Barma ya aiko:

Your browser doesn’t support HTML5

Dambarwar Siyasa Kan Takarar Alassan Ouattara