Magoya Bayan Shigowar Baki Za Su Yi Zanga-Zanga Yau a Amurka

  • Ibrahim Garba

Wata zanga-zangar magoya bayan shigowar baki Amurka

A cigaba da nuna rashin amincewa da manufofin Shugaba Trump kan shigowar baki, kungiyoyin magoya bayan kaurar jama'a daga kasa zuwa kasa za su yi zanga-zanga yau a fadin Amurka.

Kungiyoyi masu goyon bayan kaurar jama'a daga kasa zuwa kasa, na shirin gudanar da jerin zanga-zanga a fadin Amurka a yau dinnan Asabar, don su nuna bacin ransu kan manufofin Shugaba Donald Trump na babu sani ba sabo game da bakin haure.

Hadakar kungiyoyi masu ra'ayin gaba-dai gaba-dai, ciki har da kungiyoyin da su ka shirya zanga-zangar mata shekaru biyu da su ka gabata, na shirin tsara yadda wasu mutane sama da 600 za su tattara dubban mutane su yi zanga-zangar a fadin kasar.

Ana kan shirya zanga-zangar ce a manyan biranen da su ka hada da Washington DC, da Los Angeles da New York da kuma sauran kanana garuruwa a fadin kasar.

Zanga-zangar ta yau Asabar, wacce aka yi wa taken, A Dunkule Iyalai Su ke, na samun kudaden gudanarwa da kuma goyon baya ne daga kungiyoyi da dama ciki har da kungiyar American Civil Liberty da MoveOn.Org.