Magoya Bayan Hosni Mubarak Sun Kai Hari Kan Masu Zanga Zanga A Alkahira

A wan nan hoto ana iya ganin mahaya kan rakuma da dawaki da ake zargin magoya bayan shugaba Mubarak ne suka kai hari dandalin Tahrir.

Jiya laraba magoya bayan shugaba Hosni Mubarak sun kai farmaki kan dandalin tahrir kan dawaki da rakuma,yayinda wasu mutanen suke jefa boma-boman wuta daga kan gine gine.

Ranar laraba magoya bayan shugaba Hosni Mubarak sun kai farmaki kan dandalin tahrir,kan dawaki da rakuma,yayinda wasu mutanen suke jefa boma-boman-wuta daga kan gine gine,a wani lamari da ya nuna cewa an shirya kai wa masu zanga zangar da ke neman ganin an kawo karshen mulkin Mubarak na tsawon shekaru 30.

Da farko ‘yan zanga zanga dake nuna kyamar gwamnati suka fara maida martani cikin lumana,amma daga bisani suka fara maida martani ta jifa da duwatsu da kuma kwalabe da aka cika da mai aka cunna musu wuta kusa da dandalin da ake kira ta ‘yanci’.Likotci sun bude wurin jinya na wucin gadi cikin wani masallaci dake kusa,inda suka yi jinyar fiyeda mutane 640 da suka jikkata.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Masar ta bada labarin an kashe mutane uku a arangamomin na jiya Laraba.

Manema labarai suka ce da farko sojoji Masar sun yi harbi cikin iska da nufin raba fadan. Amma galibi rundunar mayakan kasar ta fi mai da hankali wajen kare muhimman wuraren tarihi da kuma amfani da ruwa wajen kashe wutar da tashi sakamakon amfani da makaman da aka hada da wuta.

Masu zanga zangar kyamar gwmnati suna zargin gwamnati Mubarak, da amfani da tsagera da kuma ‘yan sandan cikin da nufin kawo karshen zanga zangar ta kwanaki tara da ba’a taba ganin irinta ba. Masu zanga zangar sun nuna bajin ‘yansanda da suka kwato daga wadanda suka kai musu harin dauke da kulake,wukake da wasu makamaki.

Tashar talabijin ta kasar ta amabci wata majiya daga ma’aikatar cikin gida tana musanta cewa da ‘yan sandan ciki a hari da aka kia kan masu zanga zangar ba.

Ahalin yanzu kuma,gwamnatin kasar Masar tana kokarin kara tabbatarwa jama’a cewa su kwantarda hankalinsu gameda fasrgaban karancinn abinci,domin an fara samun layuka masu yawa a gidajen burodi d a kuma manyan kantunan zamanai a babban birnin kasar Alkahira.