Maganin Tawaye, 'Yan Sandan Jahohi, Inji Sarkin Musulmi da Gwamna Wamakko

Sarkin Musulmi Muhammadu Saad Abubakar III.

Sarkin Musulmi yayi wannan magana ce lokacin da ya kaiwa gwamna Wamakko gaisuwar Sallah.

Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar III da gwamnan jahar Sokoto Aliyu Wamakko sun bayyana goyon bayan ra'ayin kafa 'yan sandan jahohi domin a shawo kan rigingimun 'yan tawaye a kasar Najeriya.

Shugabannin biyu sun tattauna ne a Sokoto lokacin da Sarkin Musulmi ya kaiwa gwamna ziyarar barka da Sallah.

Your browser doesn’t support HTML5

Manyan Arewa sun fara neman a kafa 'yan sandan jahohi.-3':10"

A can baya dai manyan kudancin Najeriya ne ke so a yi 'yan sandan jahohi, a yayin da manyan arewa suka nuna dari-dari a lokacin.

Sarkin Musulmi ya ce yanzu ne lokaci mafi dacewa na samar da 'yan sandan jahohi, ya kara da cewa yin hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron da ake fama da su a wasu sassan kasar. Kuma ya ce hakan zai taimakawa 'yan sandan gwamnatin tarayya wadanda yanzu haka ake turawa jahohin da ba na su ba.

Wakilin Sashen Hausa a Sokoto Murtala Faruk Sanyinna ne ya aiko da rahoton.