Masana kimiyya sun bayar da sanarwar wani gagarumin nazarin da ya gano cewa wani maganin kashe kaifin cutar kanjamau, watau SIDA, yana iya yin rigakafin kamuwa da wannan cuta a tsakanin wasu mazaje ‘yan luwadi da aka nazarce su.
Cibiyar Harkokin Kiwon Lafiya ta Amurka, wadda ta gudanar da nazarin, ta gano cewa wannan maganin kashe kaifin cutar kanjamau mai suna TRUVADA, yana rage kasadar kamuwa da cutar baki daya da kashi 44 cikin 100 a tsakanin maza masu neman maza. Cibiyar ta ce ga wadanda suke shan wannan magani kusan kullum kamar yadda likitoci suka bukace su a nazarin ma, kashi 73 cikin 100 ne suka samu kariya daga kamuwa da cutar.
An wallafa sakamakon wannan nazarin ne cikin mujallar harkokin kiwon lafiya mai suna "New England Journal of Medicine."
Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana sakamakon wannan nazarin a zaman mai matukar muhimmanci, wanda zai haifar da wani sabon babi wajen rigakafin kamuwa da kwayar cutar HIV mai haddasa SIDA ko kanjamau. A cikin wata sanarwar da ya bayar, shugaban na Amurka yace a yayin da ake ci gaba da wannan nazari, yana da matukar muhimmanci kuma a ci gaba da yin amfani da muhimman hanyoyin da aka sani aka kuma tabbatar da amfaninsu a yanzu haka na gujewa kamuwa da wannan cuta.
Dr. Anthony fauci na Cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa ta Amurka yace an gudanar da wannan nazarin ne kawai a tsakanin maza masu neman maza, saboda haka a yanzu ba za a iya cewa lallai zai iya shafar wasu jinsunan ba. Yace tilas a ci gaba da gudanar da bincike domin a ga ko maganin zai iya rigakafin kamuwa da wannan cuta a tsakanin mazan dake tarawa da mata.