Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Yaki Da Cutar SIDA Ko Kanjamau Ta Duniya


Jan kyalle na nuna goyon baya ga yaki da cutar SIDA ko Kanjamau da aka daura a kofar fadar shugaban Amurka ta White House, talata 30 Nuwamba, 2010
Jan kyalle na nuna goyon baya ga yaki da cutar SIDA ko Kanjamau da aka daura a kofar fadar shugaban Amurka ta White House, talata 30 Nuwamba, 2010

Asusun UNICEF yace yin gwaji da jinyar da ta hada da bayar da magunguna masu dakushe kaifin kwayar cutar HIV, zasu iya hana kusan dukkan mata masu ciki bayar da kwayar cutar ga jariran da zasu haifa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana iya kaiwa ga zuriyar da ba zata fuskanci cutar SIDA ko kanjamau nan gaba a duniya ba, muddin dai kasashen duniyar zasu kara kaimin samar da hanyoyin kare kai daga kwayar cutar HIV, da jinyar wadanda ke da ita, da kuma kyautata rayuwarsu.

Sanarwar da Asusun Tallafawa Yara na majalisar, UNICEF, ya bayar jiya talata, ta ce miliyoyin mata da yara a kasashe matalauta dake dauke da kwayar cutar HIV sun kasa samun kulawa a saboda jinsinsu, ko nauyin aljihunsu ko ilminsu.

Wata ma'aikaciyar jinya tana ba wani jariri mai fama da cutar SIDA magani a birnin Durban a Afirka ta Kudu, talata 30 Nuwamba 2010
Wata ma'aikaciyar jinya tana ba wani jariri mai fama da cutar SIDA magani a birnin Durban a Afirka ta Kudu, talata 30 Nuwamba 2010

Amma kuma babban darektan asusun na UNICEF, Anthony Lake, yace yin gwaji da jinyar da ta hada da bayar da magunguna masu dakushe kaifin kwayar cutar HIV, zasu iya hana kusan dukkan mata masu ciki bayar da kwayar cutar ga jariran da zasu haifa.

An wallafa wannan rahoto jiya talata, jajiberen ranar cutar SIDA ta duniya. Yau 1 ga watan Disamba aka tsaida a zaman ranar da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a fadin duniya suke yayata hanyoyin gwaji tare da kare kai daga cutar SIDA ko kanjamau.

A yau laraba shugaba Barack Obama na Amurka zai yi magana a wajen wani bukin ranar Kanjamau ta Duniya a Washington, yayin da a jiya talata aka makala wani jan kyalle na nuna goyon baya ga yaki da cutar a kofar shiga fadar White House.

XS
SM
MD
LG