Yayin da rashin zaman lafiya ke ci gaba da addabar wasu yankunan arewacin Najeriya, wasu al’umomi a jihar Taraba sun dauki matakin shawo kan lamuran tsaro, ta hanyar hada taro da sisi don daukar nauyin mafarauta sun tunkari lamarin.
Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar ‘yan bindiga dake kai wa al’umomin yankunan hare-hare, baya ga haddasa asarar rayuka, su kan kwashi dukiya ko barnatawa tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.
A yunkurin neman dawo da zaman lafiya kungiyar hadin gwiwar mafarauta da ‘yan banga, an sama da ‘yan bindiga talatin a yankin Garbabi dake karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba.
Ku Duba Wannan Ma Har Yanzu Ba Mu San Yadda Tsarin eNaira Ke Aiki Ba – ‘Yan KasuwaAlhaji Ibrahim Nanaye sarkin Fulanin Garbabi, shi ne ya jagoranci aikin kawo karshen ‘yan bindigar, ya ce baya ga kashe sama da talatin sun tarwatsa wani sansanin ‘yan bindigar da su ka hana mazauna yankunan zaman lafiya.
Hakimin garin Garbabi, Salihu Abbas Muhammad, ya tabbatar da cewa ba za su zauna ba har sai zaman lafiya ya dawo, dalilin da ya sa kenan suka tashi tsaye don kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar baki daya.
Mazauna yankin sun nuna farin cikinsu game da aikin hadin gwiwar da yanzu haka yake samar da sakamako mai kyau.
Saurari cikakken rahotan Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5