Madugun yan adawan kasar Kenya Raila Odinga da jami’iyarsa ta National Super Alliance ( ko kuma NASA) ta kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi na watan Oktoban bara, ya sha alwashin gudanarda bikin rantsar da kansa a matsayin sabon shugaban kasa a karshen wannan watan na Janairu, idan ba a zauna aka tattauna tsakaninsa da shugaba Uhuru Kenyatta ba.
A wata hirar talbijin da yayi da sashen Swahili na Muryar Amurka, Odinga yayi watsi da sukar da ake masa na cewa barazanar nada kansa a ranar 30 ga watan Janairu da yake yi, wata dabara ce ta neman a tattauna da shi a kan raba ikon kasa da shugaba Uhuru Kenyatta.
Sai dai kuma duk da irin kalamai masu tsauri da yake yi, Odinga yace yan adawa na bukatar tattaunawa da jami’iyar Jubilee mai mulkin Kenya.
Yace suna son su tattauna ne a kan muhimman abubuwa guda biyar da shugaban na Kenya kamar gudanar da zabe bisa adalci, da tabattarda ‘yancin ma’aikatun shara’a, da yi wa ma’aikatun ‘yansanda gyaran fuska, da da inganta hanyoyin gudanarda iko da kuma sake tsarin shugabanci a cikin kundin tsarin mulkin kasar.