Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Kenya Ta Amince Da Nasarar Zaben Uhuru Kenyatta.


Kotun Kolin kasar Kenya ta amince da nasarar zaben Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ya lashe zabe da kashi chasa'in da takwas cikin dari na kuri'u da aka kada. 'Yan adawa sun kauracewa zaben.

Kashi talatin da tara cikin dari na mutane milliyan 19.6 da suka yi rejista ne suka fito don zaben, kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta yayi bayani.

Madugun 'yan adawa, Raila Odinga, wanda ya janye daga takara a maimaicin zaben shugabancin kasar, yayi kira ga goyon bayansa da su ma su kauracewa zaben, yayin da 'yan zanga zanga suka hana a bude wasu rumfunan zabe a yankunan da 'yan hamayya suke da karfi. Odinga ya kira zaben a zaman shirme ko jeka-na-yika.

Soke zaben da aka yi cikin watan Agusta, shine karon farko da wata kotu a Afirka ta rusa zaben shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG