Madagascar Ta Aika Wa Nijar Tallafin Maganin Coronavirus

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijar sun karbi wani rukuni na tallafin maganin gargajiyar da kasar Madagascar ta ba da sanarwar hadawa a kwanakin baya domin riga-kafi da kuma warkar da cutar Coronavirus.

Hakan na cikin yunkurin da ake yi na neman hanyoyin murkushe annobar wacce ke ci gaba da lakume rayukan jama’a a duk fadin duniya.

Gomman kwalayen maganin cutar COVID-19 din da Jamhuriyar ta Nijar ta bukaci samu daga kasar Madagascar sun iso filin jirgin saman Yamai ne a ranar Talata.

Kwallayen maganin

Da yake karbar wannan tallafi, mataimakin ministan kiwon lafiyar al’uma, Anar Ismael ya bayyana cewa yawan magungunan da suka shigo hannu a halin yanzu zai ba da damar kula da mutane a kalla 900.

“Maganin da aka aiko mana zai taimaka wajen yi wa mutane 600 riga-kafi, ya kuma warkar da mutum 300.”

Kasashen yammacin Afrika sama da 10 ne aka bayyana cewa sun nuna sha’awar samun sabon maganin gargajiyar na kasar Madagascar da nufin takawa wannan annoba ta coronavirus birki, abin da ya sa kasar Equatorial Guinea ta amince ta dauki nauyin dakonsa har gida.

Bayanan gwaje-gwajen da aka gudanar a ‘yan kwanakin na nuna alamun cewa Jamhuriyar Nijar ta fara shawo kan wannan annoba inda a fili ake ganin yawan wadanda suka warke ya zarta na wadanda ke kwance a asibiti a halin yanzu.

Sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a kasar ta fitar na baya-bayan nan ta ce mutum 182 ne ke kwance a halin yanzu sanadiyyar cutar COVID-19 yayin da mutum 543 suka samu waraka daga wannan cutar.

Ta kuma hallaka mutum 38 a kasar.

Saurari rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Madagascar Ta Aika Wa Nijar Tallafin Maganin Coronavirus