Yankin Madagali shine yankin da ya soma fadawa hannun mayakan Boko Haram a jihar Adamawa, kuma wannan ne karon farko da al’ummomin yankin ke gudanar da irin wannan biki na musamman domin nuna farin cikinsu game da samun zaman lafiya, da aka yi a yankin biyo bayan kwato yankin daga yan bindiga masu tada kayar baya da dakarun Najeriya suka yi.
Bikin ya hada da hawan daba, raye-rayen gargajiya da kuma addu’o’i na musamman.
Da suke gabatar da jawabai sarakuna da shugabanin addini a yankin, sun yaba game da rawar da dakarun Najeriya da kuma yan sakai suka taka, na ganin an kawar da ‘yan Boko Haram daga yankin.
Tun farko da yake jawabi shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Mohammad, ya ce an shirya bikin ne don nuna farin ciki game da nasarorin da aka samu a yanzu, tare kuma da kawo fahimtar juna a tsakanin al’umomin yankin, biyo bayan abin da wannan tashin hankali ya jawo, inda ko ya yabawa shugaba Buhari da gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindow Umar Jibrilla bisa wannan nasara.
Wannan biki dai na zuwa ne yayin da akan samu harin sari-ka-noke a wasu yankunan da aka kwaton, batun da ‘dan majalisar wakilai mai wakiltar Michika da Madagali Mr Adamu Kamale ke kira da a ‘kara kaimi.
An dai kamala bukukuwan cikin koshin lafiya duk da yunkurin da wasu ‘yan Boko Haram suka yi na kai hari, yunkurin da dakarun Najeriya suka tarwatsa.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5