WASHINGTON DC, —
Ranar Litinin 3 ga watan Disamba 2018, ta kasance wata rana da tarihi a bangaren wasan kwallon kafa ajin Mata ba zai taba mancewa da itaba.
A ranar ce ‘yar wasan gaba ta kasar Norway mai suna Ada Hgerberg ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan kwallon kafa ta bana, wadda kuma ta kafa tarihi, itace ta soma lashe kyautar Ballon d’Or ajin mata, kasancewar daga kanta aka soma bayar da wannan kyauta wa Mata.
'Yar wasan Hegerberg ta lashe kyautar ne, bisa la’akari da irin muhimmiyar gudunmawarta da ta bayar wajen samun nasarar kungiyarta ta Olympicos Lyon, dake kasar Faransa ta lashe gasar zakarun Nahiyar Turai ajin Mata.