An gargadi manyan kungiyoyi kwallon kafa kan batun takaita bayar da 'yan wasansu aro zuwa wasu kulob. Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana daya daga cikin manya manyan kulob da ake jan kunnansu, dan gane da takaita fitar da 'yan wasa zuwa wata kulob a matsayin aro.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA tace lokaci yayi da zata fara sabon tsari kan wannan lamari, inda ta shaida wa kulob din cewar zata kaddamar da wannan dokar kafin kakar wasan 2020/2021.
Bincike ya nuna cewar kungiyar Chelsea ita tafi duk wata kungiya mai buga gasar firimiya lig a kasar Ingila yawan 'yan wasa a waje, tana da adadin 'yan wasan 39 wanda ta tura so aro, zuwa wasu kulob daban daban.
A kwanannan ne dan wasan Chelsea Jamal Blackman ya dawo jinya daga kungiyar kwallon kafa ta Leeds United, inda yake zaman aro, akwai kuma Tammy Abraham, wanda yaci kwallaye hudu wa Aston Villa a ranar laraba da ta gabata shima yana zaman aro a kulob din.
FIFA tace zata amince da cewar 'yan wasa shida ko takwas ne kawai za'a yarda kulob ya fitar dasu aro a lokaci guda.
In har an bayyana wannan dokar a hukumance ya zamo dole Chelsea zata dawo da 'yan wasanta guda 30 daga kungiyoyin da suke zaman aro.
Facebook Forum