Na sha gwagwarmaya daga wajen samarin unguwa lokacin da na bude makarantar islamiyya a lokacin da nake kuruciya sakamakon suna ganin ni mace ce karama har na kai ga matsayin bude makaranta inji wata mace mai kamar maza.
Malama Sakina Isa Idris, ta ce baya ga wannan ta fuskanci gwagwarmaya da dama duba da yadda duk da takurar da ta fuskanta bata yi kasa a gwiwa ba ta hanyar jajircewa da cika burinta, sakamakon tsangwaman da ta sha hakan bai kashe mata gwiwa ba, sai ma kara mata kaimi da yayi don cika burinta na malamar makaranta.
Malama Sakina, ta ce daga lokacin da ta san malamar makaranta zata zama tun tana ‘yar shekara 9 da haihuwa, bayan mahaifiyarta ta dawo daga aikin Hajji, ta tara kawayenta domin gudanar da karatu na farin cikin dawowar mahaifiyar ta daga nan ne maulidin ya kayatar da ita a wannan lokaci sai ta bude makaranta ta koyawa kananan yara karatu.
Sakina, ta kara da cewa da taimakon wani malami wanda ake kira malam Khamalu, wanda ya mara mata baya har ta bude makaranta, da tafiya tayi tafiya har ta kai ga kammala karatunta na gaba da sakandire.
Your browser doesn’t support HTML5
Daga karshe ta ce a halin yanzu tana da malamai sun fi su talatin dake karkashin kulawarta na makarantun da ta bude, kuma ta bukaci mata daga karshe su tsaya neman ilimi sannan su taimaka wajen cigaban al’umma.