Kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana cewa zai ci gaba da bincikensa don gano ko kwamitin kamfen din shugaban kasa Donald Trump ya hada kai da kasar Rasha wajen sauya alkiblar zaben Amurka na shekarar 2016, yayin da ke gargadin cewa katsalandan din Rashar zai iya ci gaba ya kuma zamo barazana ga zabbukka masu zuwa.
Shugaban kwamitin,Richard Burr ‘dan jam’iyyar Republican daga jihar North Carolina, yace, “Har yanzu maganar katsalandan din zaben tana nan.”
Duk da yake basu fitar da wasu bayanai ba kan alakar mukarraban shugaba Trump da binciken ba, shugabannin kwamitin Richard Burr da Mark Warner, sunce sunga ya dace su fito su bayyana abin da suka gano izuwa yanzu a binciken da suke gudanarwa.
Yawancin manyan jami’an harkokin tsaron kasa na Trump sun amince da sakamakon da kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan ya samu, na cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shekarar da ta gabata, ta kuma taimakawa Trump a zaben. Sai kuma shugaba Trump bai amince ba.