Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace tana nazarin al’amura a kasar Sudan bayan shugaban kasar Omar Al Bashir ya bada umarnin nan take a sako dukkan fursunonin siyasa daga gidan yari.
Kamfanin dilancin labarun Sudan da ake kira SUNA a takaice ne ya bada labarin umarnin sako fursunonin. To amma wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa ya zuwa tsakar ranar jiya Talata goma ga wannan wata na Afrilu, babu wani tabbaci da aka samu na sako fursunonin.
Ofishin jakadancin Amurka a birnin Khartoum yana tuntubar iyalan wadanda aka sakon, domin jin halin da ake ciki.
Kamfanin dilancin labarun Sudan ya bada labarin cewa, bada umarnin sako fursunonin wani bangare ne na yunkurin inganta sasantawa da samun zaman lafiya makoni bayan da gwamnatin kasar tayi ta kamen, fada kan mai uwa da wabi domin dakile zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati.
Rahoton bai baiyana yawan fursunonin da aka bada umarnin a sako ba.