Ma'aikatan sun shiga zanga zanga ne da yajin aiki da zaman durshen akan korafin cewa ba'a kula dasu ba kuma ba'a jin kokensu.
Da sanyin safen jiya ma'aikatan suka rufe ofisoshinsu tare da kirawo manema labarai domin shaida masu dalilan da suka sa har suka tsunduma cikin yajinaiki.
Malam Muhammed Buba daya daga cikin jagoran masu yajin aikin yace abubuwa da yawa sun yi zafi. Watanni goma da suka gabata sun tafi yajin aiki saboda bukatun da suka gabatar ba'a kula dasu ba. Kullum suna fada a kansu.
Abubuwan sun hada da halayen wadanda suke aiki cikinsu. Halayensu ba na kwarai ba ne. Na biyu batun bada izinin aiki. An ba wata kungiya wata kuma an hana mata. Hakan bai cancanta ba. Ma'aikatan zasu kwashe kwanaki biyu suna zaman durshen a ofishin ministan da duk ofisoshinsu dake cikin kasar ta Niger.
Malam Muhammed Buda yace yin hakan nada matukar tasiri domin yajin aikin na kwana biyu kawai zai jawo asarar kudade da dama. Za'a samu cikas a wasu alamuran kasar.
A nata bangaren babban mataimakin magatakardan ofishin ministan makamashi ya tabbatar wa 'yan jarida cewa ma'akatan sun yi gaggawar tsunduma yajin aiki kawai ne alhali kuwa suna kokarin warware matsalolin da su ma'akatan suka ce suna fuskanta.
Malam Hassan Garba babban mataimakin magatakardan ofishin ministan makamashi da man fetur yace sun tattauna suna kuma tattaunawa da ma'aikatar kudi domin a samu fahimta tsakaninsu. Nan da 'yan kwanaki biyu ko uku za'a samu sasantawa.
Ga rahoton Abdullahi Manmam Ahmadu.
Your browser doesn’t support HTML5