Da kamfanonin jigilar alhazan sun sanar zasu fara tashi daga ranar 8 zuwa 13 ga wannan watan.
Duk kokarin da mahukunta suka kayi wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta a aikin hajji abun ya cutura. Yanzu haka maniyatta daga sassa daban daban cikin kasar sun fara isowa birnin Niamey domin mafi yawansu daga nan ake kwasarsu zuwa kasa mai tsarki. Da wuya a soma jigilarsu cikin awowi kalilan kamar yadda aka yi masu alkawari.
Alhaji Salisu Rabiu daya daga cikin shugabannin kamfanonin dake sufurin alhazan yace zancen cewa zasu tashi nan da 'yan awowi bai ma taso ba domin sai an aiko masu wasu takardu kasar daga Makka sun sa cikin fasfo din mutanen da zasu tafi kafin a soma jigilarsu. Wannan takardar ita ce zata tabbatar cewa kowane alhaji yana da wurin sauka a kasar Saudiya.
Bayan ire-iren wadannan matsalolin akwa wasu kuma da mutane suna kokawa akansu. Akwai matsalar hawa-hawar farashin kujerar hajji inda kowace shekara farashin na tashin goran zabi.
Alhaji Usman Muhammed daraktan kamfanin Baitul Islam daya daga cikin kamfanonin aikin hajji dake zaman kansu a Niger yace laifin tsadar kujera ya rataya ne akan hukumar alhazai ta kasar. Yace yau fiye da shekara goma ke nan da suke aikin amma basu taba ganin inda aka ce kujerar zuwa hajji zata kama miliyan biyu da rabi kudin kasar ba. Wannan haramun ne kuma an cuci alhazai domin su ba zasu karbi kudin da ya wuce miliyan biyu ba har da kudin abinci. Shin wadanne irin alhazai ne har za'a karbi miliyan biyu da rabi. Laifn na kan hukumar alhazai domin ita ce ya kamata ta sa ido ta tsara komi ta tabbatar ba'a cuci kowa ba.
Alhaji Bello Garba shugaban hukumar Alhazai ta kasa yayi karin haske. Akan ranakun da aka bayar da na tashi yace na wucin gadi ne domin akwai wasu ka'idodi da sai an cikasu.
Ga rahoton Abdullahi Manman Ahmadu.