Ma'aikatan Kiwon Lafiya Sun Gudanar Da Kyamfe Na Yaki Da Polio A Darazo, Jihar Bauchi

Mai Martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, shugaban kwamitin yaki da Polio na Jihar Bauchi

Jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya da na jihar Bauchi sun gudanar da aikin a bayan da aka gano cewa an tsallake wasu yara a kyamfe na baya
Ma'aikatan kiwon lafiya a Jihar Bauchi dake arewacin Najeriya, sun gudanar da wani gangamin bayar da maganin rigakafin cutar shan Inna, ko Polio, a yankin karamar hukumar Darazo dake iyakar Jihar Bauchi da johihin Gombe da Yobe.

Jami'in Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, Dr. Nuhu Barau Ningi, yace sun gudanar da bincike suka gano cewar a zagayen baya na rigakafin Polio da aka yi, an tsallake kimanin kashi 10 cikin 100 na yaran da ya kamata a ba su wannan maganin. Don haka ne yace tilas a gudanar da wannan sabon gangami na musamman da nufin tabbatar da cewa ba a ba wannan kwayar cuta sukunin yaduwa ko bulla ba.

Shugaban majalisar karamar hukumar ta Darazo, Alhaji Kabiru Adamu Sade, ya bukaci jama'a da su bayarda hadin kai domin tabbatar da an ja burki ma wannan cuta.

Wakiliyar Muryar Amurka, Amina Abdullahi Girbo, ta aiko da karin bayani daga Bauchi...

Your browser doesn’t support HTML5

Kokarin yaki Da Polio A Darazo Jihar Bauchi - 1'51"