Sultan na Sokoton ya bayyana wannan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki kan yaki da Polio a Jihar Sokoto, wanda aka gudanar a garin Kware, hedkwatar karamar hukumar Kware.
Hakimin Yabo, Alhaji Muhammadu Maiturare, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi a wannan taron, yace an hada kawunan mahalarta ne domin gano dalilan da suka sanya wasu kananan hukumomin jihar bas u tabuka abin kirki ba a zagayen karshe na gangamin rigakafin Polio da aka gudanar cikin watan Disamba.
Yace ba eai an hallara “domin dora laifi a kan kowa ba ne” dangane da gangamin. Maimakon haka yace an hallara ne domin nazarin inda aka fi karfi, da inda ke bukatar Karin karfi domin samun nasarar wannan kokarin.
Shugaban majalisar karamar hukumar Kware, Alhaji Abubakar Zamau, ya yaba ma Sultan din saboda kafa wannan kwamiti. Yace ita ma karamar hukumarsa zata karfafa wannan yunkurin ta hanyar samar da kayan aiki na tabbatar da nasarar rigakafin.