Kamar yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka shaidawa wakilin Muryar Amuraka Ibrahim Abdul’aziz, sunce yanzu watanni Uku kenan ba a biyasu albashi ba gashi kuma wata na Hudu zai shiga. Wasu daga cikin su sunce an kwashe shekaru 12 ba tare da karin matsayi ba.
To sai dai wannan zanga-zangar ta sami goyan bayan wasu kungiyoyi a jihar, Kwamarad Muhammad Abba, wanda yake shugaban kungiyar ma’aikatan jinya na babban Asibitin Tarayya dake Yola wato FMC Yola, wanda ya nuna rashin jin dadinsa ga rashin biyan ma’aikatan kananan hukumomi albashi, duk da yake yace su ma’aikatan Tarayya basu da wannan matsala.
Shugaban hadakar ma’aikatan jinya reshen jihar Adamawa, Kwamarad Jarmai, ya zargi gwamnatin jihar da nuna shakulatin bangaro game da halin da suke ciki a yanzu, inda yace baya ga rashin biyan su albashi da rashin kara musu matsayi wasu lokutan akan hada albashin watanni kafin a biya.
Sai dai kuma shugaaban hukumar kula da ayyukan jinya na jihar Adamawa, Dakta Abdullahi Belil, yace ba ma’aikatan jinya bane suke wannan zanga-zangar, yan kungiya ne na ma’aikata domin ma’aikata sun san abinda ake fama da shi. Yace yan kungiyar ne suka ki a zauna domin yin jarjejeniya. Amma dai ya tabbatar da cewa ba a biya ma’aikatan albashi ba har na tsawon watanni Uku.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5