Ma’aikatar Tsaron Jamus Ta Dakatar Da Wallafa Bayanai A Dandalin X

A makon da ya gabata, ayarin fiye da jami’o’in Jamus 60 suka bayyana cewa sun juyawa dandalin baya.

A yau Laraba, ma’aikatar tsaron Jamus ta bayyana cewar ta dakatar da ayyuka a dandalin sada zumunta na X, wanda ake zargi da yada bayanan karya karkashin jagorancin mamallakinsa Elon Musk.

Ma’aikatar tace “anan gaba ba zata sake yin zumudin wallafa bayanai a dandalin ba,” inda ta kare matsayin da cewar “musayar bayanan gaskiya na kara yin wuya” a dandalin.

Ma’aikatar ce ta baya-bayan nan a jerin hukumomin gwamnatin Jamus da suka sanarda dakatar da harkokinsu a dandalin koma suka barshi gaba daya.

A makon da ya gabata, ayarin fiye da jami’o’in Jamus 60 suka bayyana cewa sun juyawa dandalin baya.

“Alkiblar da dandalin ke kai ta sabawa muradan da cibiyoyin da ake magana ke kai-na bayyana duniya abubuwan da suke yi da martabar ilimin kimiya da rashin kunbiya-kunbiya da kuma mahawara ta dimokiradiya,” a cewarsu.

Ma’aikatar tsaron Jamus tace “tana da damar ta yi martani a kan dandalin X akan wasu kebabbun al’amura, kamar yin martani a kan labaran karya.”

Ta kara da cewa nan gaba za ta rika yin amfani ne da wata kafa dake kan dandalin WhatsApp, wacce take mallakin kamfanin Meta na Amurka mai hamayya da X, wajen yada bayananta.