Tawagar ma’aikatan Gidan Radiyon Muryar Amurka a karkashin Jagorancin Hajiya Medina Dauda, ta kai ziyarar ta’aziyya gidan abokin aikinta, marigayi Alhaji Ibrahim Abdulaziz a garin Yola.
WASHINGTON, D.C. —
A jawabin da Hajiya Medina Dauda ta gabatar a madadin sauran abokan aikin a Najeriya da kuma sauran kasashe, ta yi Addu’ar Allah ya gafatar ma marigayi Ibrahim Abdulaziz.
Daga bisani kuma Alhaji Aliyu Mustaphan Sokoto ya zanta da iyalan marigayi, Alhaji Ibarahim Abdulaziz da kuma babban dansa Abdulziz.
Marigayi Ibrahim Abdulaziz ya gamu da ajalinsa ne a sanadiyar hatsarin mota da ya rutsa da shi akan hanyar Alkaleri zuwa Bauchi a Najeriya.
Ya kasance wakilin Muryar Amurka da ke aika rahotanni daga Adamawa da Taraba.
Jama'a da dama musamman abokan aikinsa, sun kwatanta shi a matsayin mutum haziki da ya kware a fannin aikin jaridar.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5