Wannan yajin aiki ne na gama gari da ama’aikatan suka yi a fadin duniya.
Daga Singapore zuwa Dublin da Sao Paulo da Brazil da kuma Pryor, da kuma Oklahoma, ma’aikatan Google sun fice daga ofisoshinsu domin kalubalantar yadda katanfaren kamfanin yanar gizon yake nuna wariya a kan batun neman lalata da mata, sun kuma bayyana matukar damuwarsu a kan wurin aikin kamfanin.
A San Francisco, inda Google yake da ofisoshi da dama, daruruwar ma’aikatan kamfanin sun taru a wata babbar kasuwar zamani inda suka yi jawabai kana suka rike kwalaye masu rubutu da dama, wani daga ciki na cewa, "Na kai kara amma aka kara mashi girma"
Zanga zangar da ma'aikatan kamfanin na Google ta biyo bayan wani rahoton da jaridar New York Times ta buga da ta bayyana zarge zargen da ake yiwa manyan shugabannin kamfanin, da suka hada da Andy Rubin, da ake yiwa lakabi da " Uban Android," wanda aka ce an bashi dala miliyan casa'in kudin sallama. Rubin ya musanta zargin da aka wallafa a jaridar da kuma yawan kudin sallamar da aka bashi.