Lukaku Ya Bar Chelsea, Ya Koma Napoli

Romelu Lukaku, dama da Antonio Conte, hagu

Kafofin yada labaran Italiya sun ce Lukaku ya saka hannu kan kwantiragin shekaru uku a kungiyar ta Napoli wacce ke taka leda a gasar Seria A.

Dan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku ya isa birnin Naples na kasar Italiya inda zai kammala kaurarsa zuwa kungiyar Napoli.

Masu lura da al’amura kwallon kafa sun ce zuwan Lukaku kungiyar zai kara mata tagomashi.

Sama da magoya bayan kungiyar ta Napoli 100 ne suka tarbi Lukaku wanda dan asalin kasar Belgium ne a lokacin da ya isa don kammala binciken lafiyarsa.

Wani masoyin kungiyar ya fadi har kasa a turmutsitsin da aka yi, kuma nan take Lukaku ya tsaya ya duka don ya taimake shi kamar yadda AP ya ruwaito.

Kafofin yada labaran Italiya sun ce Lukaku zai saka hannu kan kwantiragin shekaru uku a kungiyar ta Napoli wacce ke taka leda a gasar Seria A.

Akan kudi dala miliyan 33 aka sayo dan wasan daga Chelsea in ji AP.