Lookman, Chiamaka Sun Shiga Rukunin Karshe Na Kyautar Gwarzon CAF

Ademola Lookman

Haka kuma tawagogin kwallon kafar Najeriya; Super Eagles ta maza da takwararta Super Falcons ta mata na cikin rukunin tawagogi 3 na karshe da aka fitar a jiya Alhamis dake neman lashe kyautar gwarzuwar tawaga ta bana.

‘Yan Najeriya 2; Ademola Lookman da Chiamaka Nnadozie sun shiga rukunin karshe na jerin ‘yan wasan da zasu fafata a gasar neman cin kyautar gwarzon dan wasan hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) a azuzuwan maza da mata.

Haka kuma tawagogin kwallon kafar Najeriya; Super Eagles ta maza da takwararta Super Falcons ta mata na cikin rukunin tawagogi 3 na karshe da aka fitar a jiya Alhamis dake neman lashe kyautar gwarzuwar tawaga ta bana.

Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan daya zura kwallaye 3 rigis a wasan karshe na gasar Europa wacce kulub din nasa ya lashe.

Abokiyar fafatawar Lookman, Nnadozie na neman lashe kambu 2 ne a gasar gwarzon dan wasan na CAF.

Akwai yiyuwar ‘yar wasar dake taka leda a kungiyar Paris FC ta ci gaba da rike kambunta na gwarzuwar mai tsaron raga ta bana a ajin mata.

Haka kuma tana cikin wadanda ke fafatawa domin neman cin kyautar gwarzuwar ‘yar wasa mace ta bana tare da Sana’a Massoudy ta kasar Morocco da Babra Banda ta Zambia.