Lokacin Lallashin Masu Daukar Makami Ya Wuce- Buhari

Taron kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya na kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alamar toshe kafar yi wa ‘yan bindiga da suka buwayi kasar ahuwa, yayinda ya bayyana cewa, gwamnati za ta ci gaba da daukar tsauraran matakai kan masu garkuwa da jama’a da kuma masu kai hare hare.

Shugaban Najeriyan ya bayyana haka ne yayin bude taron gwamnoni da sarakunan gargajiya na jihohin arewacin kasar, da kuma wakilan gwamnatin tarayya kan harkokin tsaro da aka gudanar a garin Kaduna.

A jawabinsa ta bakin babban jami’in gudanar da ayyuka na fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, shugaba Muhammadu Buhari ya ce lokaci ya yi da za a dauki masu aikata miyagun laifuka a matsayin miyagu ba tare da alakanta su da wata kabila ba.

Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga

Shugaba Buhari yace kalubale da kasar ke fuskanta na maida hannun agogo baya a kokarin gwamnati na shawo kan matsalolin talauci da koma bayan tattalin arziki, da al’ummar kasar ke fama da su. Ya kuma sanar da cewa, ya umarci shugabannin harkokin tsaro su nemi hanyar kawo karshen miyagun ayyuka a kasar.

Shugaba Buhari ya ce gudanar da wannan taron ya dace, kasancewa ana yi ne a daidai lokacin da kasar ke samun ci gaba a yunkurinta na tunkarar kalubale da ake fuskanta na inganta rayuwar al’umma da samar da muhimman ababan jin dadin rayuwa. Ya kuma shawarci jami’an tsaro su samar da sabbin dabarun shawo kan masu aikata miyagun laifuka da suke tada hankalin al’umma. Su kuma dauki matakan ba sani- ba sabo kan mahara, da masu garkuwa da jama’a da suka buwayi al’umma.

Fulani masu garkuwa da mutane

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Sokoto, Aminu Tambuwal, na Nassarawa, Abdullahi Sule, gwamnan Plato, Simon Lalong , gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da kuma gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru. Yayinda mataimakan sauran gwamnonin arewacin kasar suka wakilce su a taron.

Taron da aka kammala a cikin daren jiya, ya sami halartar Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, da Shehun Borno, Umar Ibn El-Kenemi, sai kuma Sarkin Ilori Ibrahim Sulu Gambari, da Etsu Nupe, Yahaya, da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, da kuma Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamali.

Taron na zuwa ne mako guda bayan garkuwa da dalibai, malamai da kuma wadandasu ma’aikatan makarantar sakandaren Kagara a jihar Naija.

Ranar 11 ga watan Disamba, mahara da ake kyautata zaton Fulani ne masu garkuwa da jama’a suka kai hari a makarantar sakandaren gwamnati dake garin Kankara a jihar Katsina su ka yi.

adadin-dalibai-mata-317-aka-sace-a-zamfara---yan-sanda

yan-bindiga-sun-sace-daruruwan-dalibai-mata-a-makarantar-sakandaren-jihar-zamfara

unicef-ta-yi-allah-wadai-da-sace-yan-mata-a-zamfara

Karin bayani akan: Shehin Malami Dr Ahmed Gumi, Muhammadu Buhari, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.