Lokacin Da Teloli Suka Fi Fuskantar Matsi a Sana'arsu

Bisa al’ada, kwanakin goman karshen watan azumin Ramadana lokaci ne da ake samun cunkoso a shagunan teloli, inda mafi yawan lokuta ake samun sabani tsakanin telolin da masu kai dinki.

Mohammad Jamil, na daya daga cikin kwastamomi da DandalinVOA ta iske a wani shagon dinki a Kanon da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya ce zuwansa na shida shagon telansa amma har yanzu ba’a gama masa dinkin ba.

Jamil ya dauki matakin kai dinkinsa da wuri, wato tun a farkon ranakun azumi domin kaucewa hakan, amma haka ba ta cimma ruwa

Ya ce ya fitar da rai a sauran dinkunan nasa tun da an shafe fiye da mako biyu ba a cika masa alkawari ba a baya bare a yanzu da aka zo gab da sallah karama.

Sai dai a bangaren telolin sun ce ba laifinsu ba ne, jikirin da ake samu wajen kammala dinkin.

Malama Wasila Adamu, wacce tela ce, ta ce laifin kwastamominsu ne da ke kai masu dinki amma ba sa ba da wani "advance" ko kuma kudin kafin alkalami, na kudin dinki.

Ta ce sukan kuma sa na su ranar da za’a dinka masu kaya bayan ba su ba da kafin alkalami ba.

Wasila ta ce duk kuwa wanda bai bayar da kudin kayansa ba lallai yana tare da rashin cika alkawarin tela na samun jinkiri domin a dinka wa wadanda suka shirya karbar na su ta hanyar biyan kudinsu tun da wuri.

Haruna Shu’ibu, shi ma tela ne, ya kuma ce rashin cika alkawarin na da alaka da tela da aka kai wa dinki.

A cewar shi, ana samun wasu lokutan da suke kuskure duba da yawan al’umma da suke kai dinkunansu a wannan lokaci.

Daga karshe ya ce abinda ya fi ci masa tuwo a kwarya shi ne rashin cikawa yara alkawari wajen kammala masu dinki amma ya ce yana kamantawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Lokacin Da Teloli Suka Fi Fuskantar Matsi a Sana'arsu