Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karuwar Sace-Sace Gabanin Sallah Son Zuciya Ko Talauci


A yayin da ake saura mako guda ga sallah karama lokaci ne da ake samun cunkoso a kasuwanni da wurare da ake hada-hadar cinikaiya ake kuma samun yawan sace-sace, akan wannan batu ne muka zanta da wasu matasa dangane da dabi’ar nan ta sace-sace a kasuwani.

Wannan lokaci ne ake yawan samun ire-iren wadannan matsaloli na sace-sace domin abin ya ci tura satar ta tashi daga kan maza a yanzu har da mata ma suna yi kuma kananan yara, lamarin da jama’a da dama suka ce son zuciya ne ke haddasa hakan.

A bangaren mata kuwa, wata mace da muka zanta da ita cewa ta yi a kan idonta an kama wata mace da ta aikata wannan dabi'a ta sata tana gaba kadan ta sai ta tarar da an sake kama wata dattijiya ita ma tayi satar da kyar wani bawan Allah ya kwatota daga hannun mutane, inda ta kara da cewar satar yanzu ba a wajen mata kadai ya tsaya ta har ma da maza suna yi.

Da dama dai daga cikin wadanda muka zanta da su sun alakanta matsalar sace-sace ne da yawan talauci da son zuciya ne ke jefa wadannan mutane zuwa ga sace-sace, kuma malamai suna ci gaba da jan hankalin mata da su kauracewa wannan dabi’a a cewarsu ba dabi’a ce da ta dace a kowacce al’umma ba.

Matasan sun ja hankalin hukumomi da a tsaurara hukunci da ake yi wa wadanda aka kama suna sace-sace ba kawai a dinga bada belinsu a kan kudade kalilan ba muddin ba'a aiwatar da haka ba, lallai matsalar sace-sace a kasuwannin zata cigaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG