Hukumar dake kula da gasar firimiyar Najeriya (LMC) taci tarar kungiyar Kwallon kafar Kano Pillars Naira Miliyan Takwas, da kuma dakatar da kungiyar daga buga wasanni Uku ba tare da 'yan kallo. (Close Door) a wasannin da zatayi na Kaka mai zuwa.
Hukumar ta kuma dakatar da Jagoran 'yan wasan kungiyar ta Kano Pillars, (Captain) Rabi'u Ali, daga buga wasanni guda Goma Sha biyu.
Hukuncin ya biyo bayan kutsawa cikin fili dakuma jefe-jefe da magoya bayan kungiyar sukayi ne a wasan da Kano Pillars din ta tashi Daya da Daya tsakanin ta da Rangers International a gasar Zaratan Kungiyoyi shida dake taka leda a Firimiyar Najeriya (Super 6) a birnin Lagos.
Hukumar tace ta dakatar da Rabi'u Ali ne bisa haura wa kan Alkalin wasa da cin mutuncin sa wanda hakan yasa sauran magoya bayan kungiyar suka shiga fili gami da nuna rashin da'a wa jami'an dake sa ido a gasar.
Hukumar tace yanzu haka kungiyar ta Kano Pillars da kuma Dan wasan nata Rabi'u Ali, na da sa'o'i Arba'in da Takwas (48) don amincewa da hukuncin ko kuma daukaka kara akan na rashin amincewa da hukuncin.