Liverpool Ta Lashe Gasar Premier

  • Murtala Sanyinna

LIVERPOOL Players

Liverpool ta kai karshen kamfar kofin gasar Premier na tsawon shekaru 30

Kungiyar kwallon kafar Liverpool ce ta lashe gasar Premier ta Ingila ta bana.

Liverpool din ta lashe gasar ne bayan da a Chelsea ta yi galaba a kan Manchester City a yau da ci 2-1, wanda ya ba da tazarar maki 23 a tsakanin Liverpool din da ke saman tebur da Manchester City da ke bin ta, wanda kuma ba za ta iya kamo ta ba a sauran wasannin da suka rage na gasar.

Fans Celebrates

Wannan ne karo na farko da liverpool din za ta daga kofin na Premier a cikin shekaru 30, tun daga shekarar 1990 da ta lashe kofin.

Kammala wasan na Chelsea da Manchester City ke da wuya, masoyan Liverpool a duk fadin duniya sun soma bukukuwa da tsallen murnar wannan gagarumar nasara a launi ja na kungiyar.

Fans Celebrates