Liverpool Ta Dare Saman Teburin Premier Bayan Lallasa Palace

Bayan wasan Liverpool da Palace

Manchester United, wacce za ta kara da West Ham United a ranar Lahadi ta koma matsayi na biyu a teburin gasar.

Liverpool ta shure Manchester United daga matsayi na farko a teburin gasar Premier League ta Ingila inda yanzu take da maki 13.

Zakarun na Anfield sun kai wannan matsayi ne bayan da suka yi wa ‘yan wasan Patrick Vieira na Crystal Palace wankin babban bargo da ci 3-0.

Duk da cewa ‘yan wasan na Liverpool sun fara da taga-taga a farkon wasan, Sadio Mane ya zura kwallon farko a minti na 43, lokacin ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan kuma an dawo daga hutun rabin lokaci ne Mohamed Salah ya kara kwallo ta biyu a minti na 78.

Sai Naby Keita ya zura ta uku gab da lokacin ya kusa cika – wato ana minti na 89.

Rabon da Liverpool ta dare saman teburin tun a watan Janairu bana.

A makon da ya gabata ita ma Palace ta lallasa Tottenham Hotspur da ci 3-0 wacce ta buga wasa da ‘yan kwallo 10 bayan da aka ba Japhet Tangangana Tottenham jan kati a minti na 58.