Liverpool Ta Daga Kofin Premier

  • Murtala Sanyinna

Liverpool

Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta daga kofin gasar Premier na bana a yau Laraba, jim kadan bayan bayan wasan da suka doke Chelsea da ci 5-3 a filin wasansu na Anfield.

Kaftin din kungiyar ta Liverpool Jordan Handerson ne ya daga kofin na farko da kungiyar ta lashe a cikinj shekaru 30.

LIVERPOOL

Liverpool din ta karbi kofin ne a filin wasan mai fadin daukar mutane 53,000 wanda ya ke wayam ba ‘yan kallo, sakamakon dokokin annobar coronavirus.

LIVERPOOL


Tun a ranar 25 ga watan Yuni ne aka tabbatar da Liverpool din a matsayin zakarun gasar ta Premier, bayan da abokan adawarsu na kusa wato Manchester City ta sha kashi a hannun Chelsea.