Lionel Messi Ya Jefra Kwallaye 500 A Tarihi

Jagorar gasar La Liga ta kasar Spain Barcelona ta sake shan kashi a wannan makon sa’ad da Valencia ta bita har gida ta doke ta da ci 2 – 1, kwallo daya da Lionel Messi ya jefa wa Barcelona ta cike kwallaye dari biyar cif (500) da ya jefa a tarihin sa na kwallon kafa, sai dai ba wata doguwar murna domin kuwa kungiyar tasu ta sha kashin ne karo na ukun a jere da juna a gasar wasan La Liga, kuma karo na hudu Kenan da take shan kashi a wasannin ta hudu data buga a jere.

Barcelona ta soma wannan watan na Afirilu ne da tazarar maki 9 a teburin gasar ta La Liga, amma kuma ta fara fuskantar koma baya tun sa’adda Real Madrid ta mayar da bashin dukan da aka yi mata a El Clasico mai zafi wanda shine farkon soma shan kashin ta, yanzu haka dai Atletico Madrid da ta fitar da Barcelona a gasar zakarun Turai a tsakiyar mako ta daidaita da ita a yawan maki wurin gasar ta La Liga bayan da ita kuma ta doke Granada da ci 3 – da nema a jiya lahadi.

Duka kungiyoyin biyu nada maki 76 ne amma Barcelona ce a sama da mafi yawan kwallaye, yayin da Real Madrid da ta lallasa Getafe da ci 5 – 1 take ta uku da maki 75, wato banbancin maki daya tal Kenan a tsakanin su, lamarin da ya kara zafafa takarar lashe kofin gasar ta La Liga yayin da ya rage saura wasannin biyar biyar a karawar.

A kasar Italiya kuma Juventus na kara matsawa a fafutukar lashe kofin gasar serie A karo na biyar jere, bayan da a karshen makon nan ta doke Parlemo da ci hudu da nema, yanzu haka dai Juventus na saman teburin gasar ne da maki 79 tare da tazarar maki 9 tsakanin ta da Napoli dake binta da maki 70, bayan da ita kuma ta sha kashi a gidan Inter Milan da ci 2 da nema.

Roma ce ta uku a cikin gasar da maki 65, bayan da tayi kunnen doki da Atlanta da ci 3 – 3.

A Ingila kuma yayin da Manchester City ta sami dagawa saman teburin Premier zuwa matakin ta uku sakamakon doke Chelsea da tayi da ci 3 da nema a karshen mako, Arsenal ta kasa damarta ta komawa matsayin na uku da take a kai.