Likitocin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki Tare da Mika Bukatu Ashirin da Hudu

Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo.

Duk da gina asibitoci da gwamnati keyi da wuya a samu isassun magunguna da kayan aiki musamman a yankin karkara.

Sanarwar dakatar da yajin aikin daga wannan makon bai sa aiki ya kankama ba a wasu asibitoci da dama na kasar.

Lamarin ba zai rasa nasaba da zuwa asibiti ba rashin biyan bukata ba inda sanadiyar yajin aikin mutane da dama suka rasa rayukansu.

Dr. Lawal Musa Tahir likitan yara a babban asibitin tarayya yace gaskiya ba zai iya sanin abubuwan da suka faru lokacin da basa bakin aiki. Kuma lokacin da suka dawo babu wani abu dake faruwa a asibitocin. Da yawa daga cikin marasa lafiya basu zo asibiti ba. Wurare da yawa babu marasa lafiya musamman bangaren kwanciya. Bai kamata abar matsalolin da suka haddasa yajin aikin su kai inda suka kai ba.

Yajin aikin da likitocin suka janye sun mika bukatu ne kusan ashirin da hudu cikinsu har da tabbatar da nada likitoci kawai a matsayin manyan daraktocin asibiti, karin hasafi da ingancin kayan aiki.

Tsohon likita Dr. Junaidu Muhammed ya bugi jaki da taiki kan yajin aikin da aka janye. Yace shi bai goyi bayan yajin aikin ba kamar yadda bai goyi bayan iskancin da ASUU, wato kungiyar malan jami'o'i, ta keyi ba kullum. Sai su shiga yajin aiki su bar yara wata da watanni ko shekaru ba karatu. Amma kuma mai hankali ba zai wayi gari ba yace ya kori likitoci 16,000 rana daya. Da wanda ya gama shekaru biyu da suka wuce da wanda ya gama shekaru talatin wai a ce duk an koresu aiki bai nuna hankali ba. Yace shi wannan matakin bai dameshi ba domin shi yana da halin da zai iya kai 'ya'yansa ko iyalansa inda ake biya a yi.

Dama can yadda ake aikin likitanci mutane masu mutunci ake dauka ba domin neman kudi ba ko neman suna ba.

Kawo yanzu dai gwamnati bata sanarda dauke matakin korar likitocin dubu goma sha shida ba. Amma mai magana da yawun gwamnati yace likitocin su jira matakin gaba yayin da masu hannu da shuni ke rugawa kasashen turai ko Indiya domin neman maganin ciwon kai. Akasarin 'yan Najeriya sun dogara ne da asibitocin gwamnati idan kuma sun fantsama yajin aiki saidai su koma gida su zubawa sarautar Allah ido.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Likitocin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki Tare da Mika Bukatu Ashirin da Hudu - 3'04"