Lura da yadda kai da kawon makiyaya daga wannan kasa zuwa waccan ke zama wata hanyar yada cututtukan dabobi a tsakanin kasashe ya sa kungiyar CEDEAO bullo da yekuwar allurar riga kafin bisashe akan iyakokin kasashe mambobinta dalili kenan bayan kammala zagayen kamfen da aka gudanar a baya bayan nan a daukacin yankin Afrika ta yamma likitocin dabbobi da wakilan kungiyoyin makiyaya su ka hadu a birnin Yamai don bitar wadannan ayyuka.
Makiyayan kasar Ghana na daga cikin wadanda ke dandana kudar cututtukan da ake hangen dakile yaduwarsu a yankin CEDEAO, wakilinsu a wannan taro Imam Hannafi Sunday ya fayyace girmar wannan matsala a kasarsa.
Tasirin riga kafin da aka shirya a baya ya haifar da walwala a wajen makiyayan da abin ya shafa saboda haka su ke ganin bukatar dorewar wannan tsari na kungiyar ECOWAS.
A cewar Souleymane Djibril wani mai halartar wannan zama daga Togo idan so samu ne zai yi kyau a fadada irin wannan tsari zuwa sauran sassan Afrika.
Taron yaki da annobar cututtukkan dabbobi da ya gudana a shekarar 2022 a birnin Abidjan ne ya bullo da tsarin kiran irin wannan haduwa ta bitar yekuwar allurar riga kafi lokaci zuwa lokaci domin kara inganta wannan tafiya ta bai daya a tsakanin kasashen CEDEAO.
A wannan karon bayan shafe kwanaki 4 na musanyar bayanai, tawagogin na likitocin dabobi da shugabannin kungiyoyin makiyaya za su bullo da sabbin shawarwarin da za a gabatar da su ga gwamnatocin kasashen Afrika ta Yamma.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5