Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki A Najeriya

ADAMAWA: Likitoci a FMC Yola sun raba tagwayen da aka haifa a manne da juna

Kungiyar likitocin Najeriya ta fara yajin aiki na sai baba ya gani a jiya litinin 2 ga watan Ogustan 2021 sakomakon rashin ciki alkawarin yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin kasar

Yajin aikin kungiyar likitocin ya zo ne kwanaki 113 bayan da ta janye yajin aikin da ta shiga a can baya, a cewar shugaban kungiyar Okhuaihesuyi Uyilawa.

Likitocin sun shiga yajin aikin ne kan korafe-korafe da suka hada jinkirin biyan albashi da alawus-alawus, karancin ma’aikata a asibitoci da kuma rashin ingantaccen yanayin aiki yayin da ake kara samun yaduwar annobar korona a kasar.

Shugaban kungiyar yace wannan karon ba gudu babu ja da baya har sai gwamnati ta biya wa kungiyar ta NARD bukatunta.

A wata sanarwa da hukumar lafiya ta kasar ta fitar kan yajin akin, Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehenire yayi kira ga kungiyar likitocin dasu sassauta don a sami warware lamarin cikin ruwan sanyi, kada a samu koma baya a aikin kiwon lafiya.

Yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kara samun masu kamuwa da cutar korona da kuma barazanar barkewar cutar cholera a wasu yankuna.