Boren cin abinci da bakin hauren ke yi a cibiyoyin da ake tsare da su, ya shiga kwana na hudu, a cewar wani mai yajin cin abinci da ya fadawa Muryar Amurka ta wayar tarho da kuma shafin sada zumunta.
Ya kuma turo da hotunan mutanen da ake tsare da su, wadanda wasunsu ke rike da wani kwali da aka rubuta cewa “muna cikin kabari” da wani rubutun yana cewa “a cece mu daga bam na gaba”.” Mune muka tsira, amma kuma har yanzu ana auna mu.”
Labaran da karin wasu hotuna na masu zanga zangar ya fito ne daga wasu da ake tsare da su ta wayar salula a asirce.
A makon da ya gabata, hare haren saman sun auna cibiyoyin tsare jama’ar da daddare, bayan da kungiyoyin kasashen duniya suka yi wani gargadi ga dukkan bangarorin biyu na Libiya da suke ci gaba da gwabza yaki cewa fararan hula na tsare a wani wuri, wanda ya auna su tun da farko.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta fada cewa akwai hujoji da ke nuna cewa wurin tsare jama’ar na kusa ne da wani rumbun adana makamai, amma hukumonin Tripoli sun ce babu wani takamaiman dalili da zai sa sojoji su auna yankin.