Leicester City Ta Yi Waje Rod Da Mai Horar Da 'Yan Wasanta

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City dake Kasar Ingila ta bada sanarwar sallamar mai horas da ‘yan wasanta Craig Shakespeare, mai shekaru 58, da haihuwa.

Kungiyar ta Leicester City tace yin hakan ya zamo mata wajibi domin mai horar da ‘yan wasan ya kasa tabuka wani abun azo a gani a matsayin sa tun da ya karbi jagoranci kungiyar watanni hudu da suka wuce.

Shakespeare ya karbi ragamar horar da ‘yan Leicester City, ne bayan da suka sallami mai horar da kungiyar Claudio Ranieri, wanda ya Lashe kofin firimiya lig na 2015/16, lokacin Shakespeare, yana matsayin mataimakinsa.

Shakespeare ya rike kungiyar a matsayin rokon kwarya daga bisani aka tabbatar masa da ya kasance cikakken mai horarwa na dindindin, a ranar 8/6/2017.

Ya rattaba hanu zai kasance a kungiyar na tsawon shekaru uku inda yayi watanni hudu kacal kungiyar ta sallameshi. a ranar talata 17/10/2017.

A shekarar 2015/16 kungiyar ta Leicester city, ta kafa tarihi inda ta lashe kofin Firimiya lig na kasar a karon farko tun da aka kafata fiye da shekaru dari.

A bana kuwa kungiyar tana mataki na goma sha takwas ne a kasan teburin Firimiyar inda ta take wasannin takwas da maki shida kacal, a ranar litinin da ta gabata kungiyar ta Leicester City, ta kara da Westbromwich a gasar firimiya lig mako na takwas inda sukayi kunnen doki 1-1.