A wani zama da ‘yan Majalisar Dokokin jihar suka gudanar ranar Litinin, akasarin ‘yan Majalisar sun bayyana bukatar tsige gwamnan da mataimakiyarsa da kuma daukar matakai na dakatar da wasu Kwamishinoni bisa zargin da ake musu na kasa gabatar da kasafin kudin bana akan lokaci.
Sai dai kakakin Majalisar Dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya roki ‘yan Majalisar da su baiwa gwamnan Karin lokaci ko kuma damar gabatar da uzurin dake gabansa, domin jin dalilan da ya sa ya kasa gabatar da kasafin.
Wannan takun saka dai ya samo asali ne ana dab da fara zabe na fidda gwani na takarar mukamin gwamna a zaben da za gudanar a watan gobe.
Daukan wannan mataki na fara shirin tsige gwamman jihar Legas dai ya samo asali ne lokacin da mataimakin kakakin Majlisar Wasu Eshilokun Sanni, ya gabatarwa Majalisar wani rahoto wanda ke da nasaba da kasafin kudin.
Wakilin Muryar Amurka a Legas Babangida Jibrin ya ji mabanbantan ra’ayoyin wasu mazauna Legas kan wannan takaddamar dake faruwa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5