Cibiyar bunkasa noman Tumatir ta Techno-serve hadin gwiwa da ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayyar Najeriya ne suka shirya taron, inda masana da manoman Tumatir da kuma jami'an gwamnati suka karawa juna ilimi kan yadda za'a habaka harkokin noman Tumatir a Najeriya.
Farfesa Mahmud Daneji, Manajan Daraktan hukumar bunkasa ayyukan noma da raya karkara ta jihar Kano mai lakabin KNARDA, ya ce duk wani abu da aka fito da shi sakamakon taron, gwamnatin Kano za ta tabbatar da ganin ta aiwatar da shi.
Hajiya Salamatu Garba shugaban kungiyar WOFAN mai tallafawa mata manoma a yankunan karkara tace taron nada alfanu ga mata manoma.
Babban Daraktan Cibiyar raya noman Tumatir ta Techno-serve a nan Najeriya Mr Larry Umunung, ya ce ana hasarar 45% na adadin Tumatirin da ake nomawa duk shekara a Najeriya.
To amma kwamishinan gona da albarkatun kasa kuma mataimakin gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf na cewa, samun jituwa tsakanin masu noma Tumari da masu sayarwa shine abin da zai taimaka wajen rage asarar da ake samu.
Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum