Jihar Legas na daya daga cikin manyan biranen da sabuwar cutar coronavirus ta afkawa tun farkon bullarta, lamarin da ya sa jihar ta dauki matakan dakile yaduwarta wadanda suka hada da rufe wuraren ibadu da kasuwanni da sauran wuraren mu’amular al’umma.
Ya zuwa yanzu dai an fara sassauta matakan kulle da aka saka domin hana yaduwar cutar, sai dai wasu na ganin ci gaba da rufe wuraren Ibada da ake ci gaba da yi, alama ce dake nuna gazawa.
Gwamnatin jihar ta saka wasu dokoki da idan ana son bude wuraren Ibada to kuwa sai an bisu, lamarin da wasu. musulmai ke ganin dokokin sun sabawa koyarwar addinai.
Musulmai da Kristoci a jihar Lagas na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da matakai masu tsauri da suke ce gwamnati ta kakaba, wanda ya hana kananan Yara ‘yan kasa da shekaru 15 ba zasu je wajen ibada ba, ko kuma duk mutnen da suka wuce shekaru 60, saboda sun fi fuskantar barazanar cutar coronavirus.
Domin cikaken bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5