Lauyoyin Trump Ba Za Su Bari Ya Amsa Tambaya Ba Akan Binciken Zargin Shishshigin Rasha A Zaben 2016

Shugaban Amurka Donald Trump

Jagoran lauyoyin Shugaban Amurka Rudy Guliani ya ce ba za su bari shugaban ya amsa kowace tambaya ba akan binciken zargin shishshigin da Rasha ta yi a zaben shugaban na shekarar 2016

Jagoran lauyoyin Shugaba Donald Trump Rudy Giuliani yace ba wani sirri bane cewa ko Trump din zai amsa tambayoyin masu binciken shisshigin da ake tuhumar Rasha tayi a zaben Amurka na shekarar 2016, amma dai abinda tawagar tayi ittifaki akai shine ba zata bar shi ya amsa ko wace tambaya ba.

Tun da jimawa Trump yace yana so ya amsa tambayoyi daga kwamitin binciken Robert Mueller, to amma a jiya lahadi sai Giuliani ya fada wa gidan talabijin na ABC cewa kusan sun cimma matsaya akan wannan batu, na hana shugaban na Amurka ya zauna domin ayi masa tambayoyi, Maimako Giuliani yace akwai yiwuwar hakan ta rutsa dashi, muddin ko aka same shi da kantara karya to wannan yana nufin wani babban laifin ne a dokar kasar da yayi rantsuwar karewa.

Giuliani dai tsohon magajin garin birnin New York ne, yace tawagar lauyoyin na Trump zasu iya barin ayi hira dashi a takaice, kuma ayi masa tambaya kai tsaye ba da wani lunge-lunge ba, yace kai wannan ma suna kokarin ganin ba ayi hakan ba.