Da alamun wannan mataki na kauracewa zaman kotu da kungiyar lauyoyin NBA, ta soma na kwanaki biyu yanzu haka ya soma jawo tsaiko a harkokin sharia, yayin da wasu lauyoyi ke ganin matakin bai dace ba.
Barista Idris Abdullahi Jalo wani lauya ne kuma dan takarar kujerar majalisar dokoki a jihar Taraba a inuwar jam’iyar APC, ya ce su basu ji dadi ba da wannan mataki na lauyoyin. Kamata ya yi kungiyar lauyoyi ta gane cewa ita kungiyace ta kwararru.
To sai dai kuma, yayin da su Idris Jalo ke sukan matakin, wasu lauyoyin na cewa idan aka bi ta barawo to abi ta mabi sawu a cewar Barista Sunday Joshua Wigra, wani lauya a Yola.
Kawo yanzu dai tuni Majalisar Dattawan Najeriya ta shigar da kara a kotun kolin kasar kan batun dakatar da babban Alkalin Alkalan, yayin da kuma ita ma Majalisar koli ta harkokin sharia a Najeriya wato Federal Judicial Council, ta kira wani taron gaggawa don duba wannan dambarwa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5