A sharhin lauya mai zaman kan sa a Abuja, Yusuf Sallau Mutum Biyu yace girman matsayin alkalin zai zama kaskanci a gare shi da jami’an shari’a in an gurfanar da shi gaban kotu ta hanyar shigar da shi akwatin ba da shaida.
Mutum Biyu yace duk da a tsarin mulkin Najeriya babban alkalin ba shi da kariya kamar ta shugaban kasa da gwamnoni, amma ya na cikin tsarin doka a bi ta hannun hukumar kula da shari’a NJC ta binciki lamarin kafin daukar matakin gurfana gaban kotu.
Da ya ke amsa tambayar matakin da kotu zata dauka in babban alkalin ya ki gurfana gaban ta karo na biyu, Barista Yusuf Sallau ya ce kotu ka iya bada sammacin kamo wanda a ke tuhuma amma ya na ganin lamarin ba zai kai ga haka ba ga babban alkalin.
Wannan dai shi ne kusan karo na farko a Najeriya da a ke yunkurin gurfanar da babban alkali kuma shugaban kotun koli gaban kotu.
Ga rahoton Nasiru Adamu Elhikaya daga birnin Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5