A taron manema labaran da ta kira Kungiyar Association des Jeunes Avocats du Niger AJAN ta fara ne da nuna takaicinta kan wasu abubuwa da dama da tace suna wakana a ‘yan makwannin nan a Nijar wadanda suka sabawa tsarin zamantakewar dukkan wata al’ummar da ke fafutika akan maganar ‘yancin bil adama da tabbatar da aiki da doka.
A hirar shi da Muryar Amurka, Me Dan Batoure daya daga cikin shika-shikan kungiyar matasan lauyoyi ta AJAN ya bayyana cewa,
"A matsayinta na mai fafutikar kare hakkin dan adam kuma wace ke son a yi komai akan gaskiya kungiyar AJAN ba za ta taba rufe ido tana kallon a na fatali da doka ba. matsalar da a yau girmanta ya kai matsayin da hatta lauyoyi ba sa samun sukunin bin diddigin mutanensu da ke hannun hukumomi."
Me Boubacar Ali shugaban wannan kungiya. Ya kuma ce"Cafke dukkan wani wanda ake zargi, abu ne da doka ta hannunta wa hukumar ‘yan sandan farin kaya ko rundunar tsaro ta jandarmomi wadanda dukkansu ke karkashin alhaki mai tuhuma wato Procureur."
Kungiyar AJAN na kiran Majalissar CNSP ta dakatar da kame -kamen mutane ba akan ka’ida ba sannan ya zama wajibi a mutunta hukuncin kotuna haka kuma dukkan mutanen da aka kama a yi masu shara’a ta adalci da gaskiya da ke bukatar a mutunta ‘yancin samun kariya.
Kwana 1 bayan da matasan lauyoyi suka fitar da sanarwa suma wasu lauyoyin na daban da ke karkashin hadin gwiwar LAWCONSULT sun bayyana damuwa a game da halin da wasu makusantan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum su kimanin 9 ke ciki wadanda ke tsare yau kwanaki a kalla 20 a ma’aikatar tattara bayanan sirri ta DGDSE cikin yanayin irin na muzantawa.
A ranar farkon juyin mulki sojojin Majalissar CNSP sun sha alwashin mutunta dukkan yarjeniyoyin kasa da kasa da Nijer ta saka wa hannu ciki har da wadanda suka shafi ‘yancin dan adam sai dai wasu ‘yan kasa na ganin ba haka abin yake ba a aikace.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5