Lauyoyi A Nijer Sun Koka Kan Rashin Samun Sukunin Gudanar Da Aiki a Kotu

NIGER: Ginin kotun Yamai

A jamhuriyar Nijer, kungiyar lauyoyi ta bayyana damuwa a game da yanayin da aka shiga a kasar bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka yi, ta bukaci bangarorin siyasa su mutunta tsarin da doka ta shimfida wajen neman hakkokin da suke zargin an tauye masu.

A wata sanarwar da suka fitar da yammacin ranar Alhamis a karkashin jagorancin shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Batonnier Me Boubacar Oumarou, lauyoyin sun fara ne da nuna rashin jin dadinsu a game da abinda suka kira tauye ’yancin aikin lauya, matsalar da ke kokarin samun gindin zama a yanzu haka a Nijer, bisa la’akari da yadda kungiyar lauyoyi ta Barreaux de l’ordre des Avocats ke samun korafe-korafen lauyoyin da ke zargin an hana masu samun sukunin kare mutanensu da aka garkame a kurkuku bayan tarzomar watsi da sakamakon zabe, yayin da suka ce matakin kulle irin wadannan mutane a gidan kaso da ke nesa da alkalin da ya kama su abu ne da ya sabawa yunkurin kusantar da jama’a da mashara’anta.

Lura da yadda cece-ku-ce ke kara tsananta a tsakanin bangarorin siyasa a kowacce safiya tun bayan fitar da sakamakon zaben 21 ga watan Fabarairu, ya sa kungiyar Barreau de l’ordre des Avocats jan hankalin ‘yan siyasa su gujewa bin son zuciya.

A tasa sanarwar da ya bayar a daren jiya ta kafar labarai mallakar gwamnati, alkali mai kare muradan hukuma a kotun birnin Yamai ya bayyana cewa ya zuwa ranar 11 ga watan Maris mutane 652 suka shiga hannun ‘yan sandan farin kaya sanadiyar zanga-zangar da aka yi fama da ita a birnin Yamai, cikinsu har da yara kanana kimanin 160 wadanda kuma aka damka 135 a hannun iyayensu. Daga cikin wadanda suka manyanta an wanke 183 yayin da ake tuhumar mutun 328 da aikata laifi daga 1 zuwa abinda ya zarce haka.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma

Your browser doesn’t support HTML5

Lauyoyi A Nijer Sun Koka Kan Rashin Samun Sukunin Gudanar Da Aiki a Kotu