Lauyan ya arce daga kasar a jiya Asabar saboda yana jin tsoro rayuwarsa bayan an saki matar a farkon wannan mako, lamarin da ya haddasa zanga zangar Musulmi a fadain kasar.
Mamabobin wata kungiyar sa kai ta Musulmi, Tehreek e-Labbaik ya Rasool Allah, sun rufe hanyoyi a manyan biranen Pakistan tsawon kwanaki uku suna bukatar a kashe alkalan kotun kolin da suka saki Asia Bibi a ranar Laraba.
Saiful Mulook shine lauyan matar mai ‘ya’ya biyar da aka yanke mata hukuncin kisa tun cikin shekarar 2010. Wasu ‘yan siyasar Pakistan guda biyu da suka yi kokarin taimaka mata, an kashe dukkansu.
Mulook ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reutuers ta sakon WhatsApp cewa ya je wata kasa ce domin ya kare rayuwarsa da na iyalinsa daga fushin jama’a. Yace ya nemi shawarwarin mutane kuma ra’ayin kowa ya zo daya, cewa ya bar kasar.
Sai dai ya kara da cewa zai dawo kasarsa ya ci gaba da aiki, bisa sharadin samun kariya daga jami’an tsaron kasar.