Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Kamfanin Google Sun Gudanar Da Zanga Zangar Gama Gari


Zanga Zangar ma'aikatan kamfanin Google
Zanga Zangar ma'aikatan kamfanin Google

Ma’ikatan kamfanin Google a fadin duniya sun yi yajin aiki domin kalubalantar yanda kamfanin ke daukar batun neman yin lalata da mata.

Wannan yajin aiki ne na gama gari da ama’aikatan suka yi a fadin duniya.

Daga Singapore zuwa Dublin da Sao Paulo da Brazil da kuma Pryor, da kuma Oklahoma, ma’aikatan Google sun fice daga ofisoshinsu domin kalubalantar yadda katanfaren kamfanin yanar gizon yake nuna wariya a kan batun neman lalata da mata, sun kuma bayyana matukar damuwarsu a kan wurin aikin kamfanin.

A San Francisco, inda Google yake da ofisoshi da dama, daruruwar ma’aikatan kamfanin sun taru a wata babbar kasuwar zamani inda suka yi jawabai kana suka rike kwalaye masu rubutu da dama, wani daga ciki na cewa, "Na kai kara amma aka kara mashi girma"

Zanga zangar da ma'aikatan kamfanin na Google ta biyo bayan wani rahoton da jaridar New York Times ta buga da ta bayyana zarge zargen da ake yiwa manyan shugabannin kamfanin, da suka hada da Andy Rubin, da ake yiwa lakabi da " Uban Android," wanda aka ce an bashi dala miliyan casa'in kudin sallama. Rubin ya musanta zargin da aka wallafa a jaridar da kuma yawan kudin sallamar da aka bashi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG