Lauya Aminu Gamawa Kan Mata Da Shugabanci

Mata suna da rawa da zasu taka mai girma a harkar siyasa da kuma shugabanci, idan aka duba kusan rabin mutanen dake Najeriya yawancin su mata ne.

Ganin iren iren matsalolin da suka shafi al’ummar kasa kamar talauci, rashin aikin yi, rashin samun kulawar kiwon lafiya, rashin ilimi na gari duk wadannan matsaloli sun fi shafar mata a wannan zamani. Daga karshe dai mata su ake bari cikin wahala, amma da zarar lokacin zabe yazo mata sun fi kowa fitowa domin su kada kuri’un su.

Haka zalika idan aka duba mataki na gida dana al’umma za’a ga a kwai rawa da mata ke takawa wajen tarbiyar al’umma da kuma nauyi da suke ‘dauka don ganin cewa an zauna lafiya an kuma sami cigaba. Amma da zarar an gama zabe sai mata suga kamar sun tura mota ne ta tashi ta bar su da hayaki, kasancewar duk abubuwan da suka shafi shugabanci mata basu da wakilci na gari.

Goyon bayan mata da taimaka musu a bangaren wakilci da shugabanci na da amfani sosai, mata nada muhimmiyar rawa da zasu taka don ganin ci gaban al’umma da kasa baki ‘daya.